Subscribe Us

Responsive Advertisement

Advertisement

Showing posts from January, 2026Show all
Cingam (Chewing gum),  abu ne da mutane da yawa ke taunawa a kullum, amma ka taɓa tambayar kanka shin yana da amfani ne ko cutarwa?Yana rage warin baki kuma yana sa baki yayi daɗi.Yana ƙara yawan miyau a baki wato (saliva) wanda ke taimakawa tsaftar baki.Yana iya ƙara taimakawa wajen rage gajiya, kuma taimakawa rage damuwa ga wasu mutane.(Sugar-free gum), wato cingam Mara sukari yana taimakawa hana rubewar haƙora.❌ Illolinsa idan an yi yawa.1..Yawan taunawa na iya jawo ciwon muƙamuƙi.2.. Chewing gum mai sukari na iya lalata haƙora.3.. Zai iya jawo kumburin ciki ko taruwar iskaWasu na iya samun ciwon ciki idan ana taunawa akai-akai.🟡 ShawaraA fi amfani da (sugar-free chewing gum)Kada a taunata kullum ko na tsawon lokaciBa zai maye gurbin goge baki ba.👉 A takaice: Chewing gum ba laifi ba ne, amma yin amfani da shi da hankali shi ne mafita.Dr. Ibrahim Al-Amana
⚠️ Illar Rashin Aski Gashin Mara (Gaban Mace ko namiji )1️⃣ Hadisin Manzon Allah (ﷺ) Kan Aski:Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Fitilar musulmi guda biyar ne: Yanke farce, aske gashin mara, askewar hammata, aske gashin baki, da yin alwala".— (Sahih Muslim 261)A wani hadisin kuma, an karbo daga Anas (RA), ya ce:"An yi mana haddi a kan aske gashin mara, aske hammata, yanke farce da gashin baki, kada mu bar su su haura kwana arba'in".— (Sahih Muslim 258)Wannan yana nuna cewa yin aski yana daga cikin tsabtace jiki da shari’a ta umarta.2️⃣ Illolin Rashin Aski Gashin Mara A Bangaren Kiwon Lafiya Ɗaukar cututtuka: Gashi na iya tara datti da gumi, wanda ke haifar da ƙaiƙayi, warin gaba, da cututtukan fata kamar ƙaiƙayin gashi (folliculitis).Warin gaba: Idan aka bar gashin mara ya yi yawa, yana hana iska ratsawa, wanda ke jawo warin gaba mai muni.Tarin kwayoyin cuta: Gashi mai yawa yana haifar da ƙwayoyin cuta da ke iya haddasa cututtuka kamar bacterial vaginosis da yeast infection.Rashin jin daɗi ga miji: A cikin aure, miji yana iya jin tsanar warin gaba ko rashin kulawa da jiki.Muna aske gashin jikin mu akai akai musamman na mara dana hammata. Dr. Ibrahim Al-Amana
Amfani fara ga mata masu juna biyu.Fara tana karin sha’awa ga ma’aurata, tana karin girman gashin kai, gashin hatta da sauran gashin jiki.kinada juna biyu kirika cin Fara, kisa asawomiki kwanon Fara (grasshopper) daya ko kwano biyu kisa a soye miki amma karki sa yaji da yawa. Kirika ci kadan kadan. Tanada amfani ga mai juna biyu. —————————————————————————Fara tana dauke da sinadarin proteins akalla tana dauke da protein yakai 70%Fara tana dauke da Mineral and vitamins wanda suka kunshi zinc, iron, vitamin A and B (riboflavin and folic acids ) da kuma magnesium.Fara tana dauke da kitse mai kyau lafiyayye wanda baya cutarwa ga jikin mutun, wanda yana daidaita yawan cholesterol acikin jini.Fara tana dauke da sinadarin Antioxidant properties Wanda Yana kariya ga lalacewar cells na dan Adam.Protein din da Fara take dauke dashi Ana converting enshi zuwa peptide wanda yana taimakawa ga saukewar hawan jini.Fara tana dauke da sinadarin dake magance matsalar Kumburi na sassan jiki.Dr. Ibrahim Al-Amana
Hanyoyin Kariya Daga Cututtukan Ƙoda:Ga wasu muhimman matakai da ke taimakawa wajen kare ƙoda:1. Shan Ruwa Yadda Ya KamataYawaita shan ruwa mai tsafta na taimakawa ƙoda wajen tace datti cikin sauƙi.2. Kiyaye Hawan Jini da SugaA rika duba hawan jini da suga akai-akai, tare da bin shawarwarin likita idan akwai matsala.3. Gujewa Shan Magunguna BarkataiMagungunan ciwo kamar diclofenac, ibuprofen, paracetamol idan ana yawaita shansu na iya lalata ƙoda.4. Cin Abinci Mai Gina JikiA rika cin kayan lambu, ’ya’yan itatuwa, da abinci mara yawan gishiri da mai.5. Rage Gishiri da Kayan MaiYawan gishiri na ƙara hawan jini, wanda ke cutar da ƙoda.6. Gujewa Taba Sigari da GiyaWaɗannan na lalata jijiyoyin jini kuma suna ƙara haɗarin cutar ƙoda.7. Motsa Jiki Akai-AkaiMotsa jiki na taimakawa wajen rage kiba, hawan jini da suga.8. Yin Gwajin Lafiya Akai-AkaiMusamman ga masu hawan jini, suga, ko tarihin cutar ƙoda a iyali. Shawara✔️ Kada a yi sakaci da lafiyar ƙoda✔️ Kada a jira sai cuta ta tsananta kafin neman magani✔️ Kariya ta fi magani Dr. Ibrahim Al-Amana