Cingam (Chewing gum), abu ne da mutane da yawa ke taunawa a kullum, amma ka taɓa tambayar kanka shin yana da amfani ne ko cutarwa?Yana rage warin baki kuma yana sa baki yayi daɗi.Yana ƙara yawan miyau a baki wato (saliva) wanda ke taimakawa tsaftar baki.Yana iya ƙara taimakawa wajen rage gajiya, kuma taimakawa rage damuwa ga wasu mutane.(Sugar-free gum), wato cingam Mara sukari yana taimakawa hana rubewar haƙora.❌ Illolinsa idan an yi yawa.1..Yawan taunawa na iya jawo ciwon muƙamuƙi.2.. Chewing gum mai sukari na iya lalata haƙora.3.. Zai iya jawo kumburin ciki ko taruwar iskaWasu na iya samun ciwon ciki idan ana taunawa akai-akai.🟡 ShawaraA fi amfani da (sugar-free chewing gum)Kada a taunata kullum ko na tsawon lokaciBa zai maye gurbin goge baki ba.👉 A takaice: Chewing gum ba laifi ba ne, amma yin amfani da shi da hankali shi ne mafita.Dr. Ibrahim Al-Amana
0 Comments