Subscribe Us

Responsive Advertisement

Advertisement

⚠️ Illar Rashin Aski Gashin Mara (Gaban Mace ko namiji )1️⃣ Hadisin Manzon Allah (ﷺ) Kan Aski:Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Fitilar musulmi guda biyar ne: Yanke farce, aske gashin mara, askewar hammata, aske gashin baki, da yin alwala".— (Sahih Muslim 261)A wani hadisin kuma, an karbo daga Anas (RA), ya ce:"An yi mana haddi a kan aske gashin mara, aske hammata, yanke farce da gashin baki, kada mu bar su su haura kwana arba'in".— (Sahih Muslim 258)Wannan yana nuna cewa yin aski yana daga cikin tsabtace jiki da shari’a ta umarta.2️⃣ Illolin Rashin Aski Gashin Mara A Bangaren Kiwon Lafiya Ɗaukar cututtuka: Gashi na iya tara datti da gumi, wanda ke haifar da ƙaiƙayi, warin gaba, da cututtukan fata kamar ƙaiƙayin gashi (folliculitis).Warin gaba: Idan aka bar gashin mara ya yi yawa, yana hana iska ratsawa, wanda ke jawo warin gaba mai muni.Tarin kwayoyin cuta: Gashi mai yawa yana haifar da ƙwayoyin cuta da ke iya haddasa cututtuka kamar bacterial vaginosis da yeast infection.Rashin jin daɗi ga miji: A cikin aure, miji yana iya jin tsanar warin gaba ko rashin kulawa da jiki.Muna aske gashin jikin mu akai akai musamman na mara dana hammata. Dr. Ibrahim Al-Amana

Post a Comment

0 Comments