Hanyoyin Kariya Daga Cututtukan Ƙoda:Ga wasu muhimman matakai da ke taimakawa wajen kare ƙoda:1. Shan Ruwa Yadda Ya KamataYawaita shan ruwa mai tsafta na taimakawa ƙoda wajen tace datti cikin sauƙi.2. Kiyaye Hawan Jini da SugaA rika duba hawan jini da suga akai-akai, tare da bin shawarwarin likita idan akwai matsala.3. Gujewa Shan Magunguna BarkataiMagungunan ciwo kamar diclofenac, ibuprofen, paracetamol idan ana yawaita shansu na iya lalata ƙoda.4. Cin Abinci Mai Gina JikiA rika cin kayan lambu, ’ya’yan itatuwa, da abinci mara yawan gishiri da mai.5. Rage Gishiri da Kayan MaiYawan gishiri na ƙara hawan jini, wanda ke cutar da ƙoda.6. Gujewa Taba Sigari da GiyaWaɗannan na lalata jijiyoyin jini kuma suna ƙara haɗarin cutar ƙoda.7. Motsa Jiki Akai-AkaiMotsa jiki na taimakawa wajen rage kiba, hawan jini da suga.8. Yin Gwajin Lafiya Akai-AkaiMusamman ga masu hawan jini, suga, ko tarihin cutar ƙoda a iyali. Shawara✔️ Kada a yi sakaci da lafiyar ƙoda✔️ Kada a jira sai cuta ta tsananta kafin neman magani✔️ Kariya ta fi magani Dr. Ibrahim Al-Amana
0 Comments